• Hariri : Isra'ila Ce Babbar Barazana Ga Kasar Labanon

Piraministan kasar Labnon Sa'ad Hariri ya bayyana haramtacciyar kasar Isra'ila a matsayin babbar barazana ga kasarsa kuma ya ce har yanzu hukumomin Isr'ailan na ci gaba da take hakkokin 'yancin kasar Labnon.

A yayin da ya halarci taron kawayen Labnon  da ya gudana a birnin Rom na kasar Italiya  jiya Juma'a, Piraministan kasar Labnon Sa'ad Hariri ya shaida manema labarai cewa kasarsa na bukatar makaman kasa da kasa domin kalubalantar barazanar haramtacciyar kasar Isra'ila.

Hariri ya ce bisa kudiri mai lamba 1701 na MDD, bisa la'akari da barazanar H. Kasar Isra'ila, wajibi ne kasar Labnon ta mallaki jami'an tsaro kimanin dubu 15, to amma a halin da ake ciki kasar ba ta da jami'an tsaro dubu 7.

Har ila yau Hariri ya yi watsi da jita-jitan cewa dakarun tsaron kasar Labnon suna bawa mayakan kungiyar Hizbullah makaman da kasashen waje suka taimaka masu da shi, inda ya ce tarihi ya nuna cewa duk  makamai da kasar Labnon ta samu yana hanun jami'an tsaron kasar ne, kuma wannan jita-jitan, kareraki ne da hukumomin haramtacciyar kasar Isra'ila ne suke watsa wa da nufin bata Sojojin kasar Labnon da kungiyar hizbullah.

Mar 17, 2018 06:26 UTC
Ra'ayi