• Mahukuntan Saudiyya Suna Ci Gaba Da Mallaka Makamai Ga 'Yan Ta'adda A Yamen

Tashar talabijin ta France 2 ta sanar da cewa: Mahukuntan Saudiyya da na Hadaddiyar Daular Larabawa suna ci gaba da mallakawa kungiyoyin 'yan ta'adda na Da'ish da Al-Qa'ida makamai a kasar Yamen.

A rahoton da tashar talabijin ta France 2 ta watsa yana fayyace cewa: Mayakan kungiyar ta'addanci ta Da'ish suna da sansani ne a wani yanki na garin Ta'az da ke shiyar kudu maso yammacin kasar Yamen, yankin da ke karkashin mamayar rundunar kawancen masarautar Saudiyya.

Tashar ta France 2 ta kara da cewa: Mahukuntan kasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa sun yi da'awar cewa suna amfani da kungiyoyin 'yan ta'addan biyu ne domin yakar 'yan kungiyar Ansarullahi ta mabiya Husi.

Tun a watan Maris na shekara ta 2015 ce mahukuntan Saudiyya suka fara kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yamen da nufin murkushe duk wata adawar tsoma bakinsu a harkokin cikin gidan kasar, inda suka kafa rundunar kawance da suka fito daga wasu kasashen Larabawa, kuma suka killace kasar ta Yamen ta sama da kasa da kuma ta ruwa lamarin da ya wurga al'ummar Yamen cikin halin kaka-ni ka yi.  

Tags

Mar 18, 2018 06:26 UTC
Ra'ayi