• Bahrain: Sabuwar Zanga-zangar Nuna Kin Jinin Gwamnati

Al'ummar Bahrain sun sake bude wata sabuwar Zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatin kasar a daren jiya asabar

Kamfanin dillancin labarun Mehriyyah ya ambato majiyar 'yan hamayyar Bahrain tana cewa; Masu Zanga-zangar sun yi tir da ci gaba da tsare babban malamin addinin kasar, sheikh Issa Kasim, kamar kuma yadda su ka bukaci ficewar sojojin mamayar Saudiyya daga kasar.

Mahukuntan kasar ta Bahrain sun raba shehin malamin da hakkinsa na dan kasar Bahrain, tun a watan Yuni na 2016, tare da tsare shi a cikin gidansa a unguwar al-Deraz.

Har ila yau masu Zanga-zangar sun yi tir da isan da jami'an tsaron kasar su ka yi wa wasu fursunoni.

Tun a 2011 ne dai kasar Bahrain take fuskantar yunkurin al'umma wanda yake nufin samar da sauyi cikin ruwan sanyi.

Tags

Mar 18, 2018 12:13 UTC
Ra'ayi