• Siriya : Turkiyya Ta Kwace Yankin Afrin

Dakarun Turkiyya da mayakan Siriya dake samun goyan bayan Ankara sun kwace daukacin ikon birnin Afrin tungar mayakan kurdawa da Turkiyyar ke kallo a matsayin 'yan ta'adda.

Shugaban kasar Turkiyyar, Recep Tayyip Erdogan, ya fada a jiya Lahadi cewa, mayakan Siriya da dakarun kasarsa sun yi nasarar kwace birnin  na Afrin, kum ayanzzu kaka tutar Turkiyya ce ke kadawa a tsakiyar yankin dake arewa maso yammacin kasar Siriya.

Wani faifan bidiyo da rundinar sojin Turkiyya ta wallafa a shafinta na Twitter, ya nuna dakarun Turkiyya kan wasu tankunan yaki biyu a gaban wasu gine gine gwamnati a yankin na Afrin.

Gwamnatin Ankara dai, na kallon kungiyar YPG ta kurdawa a matsayin kungiyar yan ta’adda, duk da cewa, dakarun kurdawan na samun nasu goyon baya ne, daga kasar Amurka, a yaki da kungiyar 'yan ta'adda ta IS a Siriya.

Daga ranar 20 ga watan Janairu da ya gabata lokacin da dakarun Turkiyya suka fara kaddamar da hari kan yankin na Afrin, dakarun kurdawa 1,500 ne aka kashe,  a yayin da Turkiyyar ta ce an kashe na ta dakaru 46 da raunana 225.

Tags

Mar 19, 2018 07:15 UTC
Ra'ayi