Mar 19, 2018 19:00 UTC
  • Saudiya Ta Bawa Kamfanin HKI Kwangilar tsaron Filin Jiragen Kasar

Masarautar saudiya ta bawa wani kamfanin aramtacciyar kasar Isra'ila kwangilar tabbatar da tsaro a filayen sauka da tashin na jirgin saman kasar

Kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto jaridar Assharq ta kasar Qatar a wannan Litinin ta wallafa cewa masarautar ali-saudiya ta fitar da wani sabon kudiri da a ciki aka bawa wani kamfanin kasar waje G4S na HKI kwangilar tabbatar  da tsaro a filayen sauka da tashin na jirgin saman kasar.

Masu sharhi kan al'amuran kasar na ganin cewa wannan kudiri da masarautar saudiyar ta dauka ya biyo bayan fargaba da tsoron da masarautar ke da shi daga bangarorin dake adawa da sauye-sauyen da masarautar ta yi a baya-bayan  nan musaman ma bayan kame wasu 'yan gidan masarautar da kuma sauke wasu manyan jami'an tsaro daga kan mikaminsu.

Har ila wasu masharhantan na ganin cewa masarautar ta dauki wannan mataki ne domin hana wasu magabatan kasar tare da taimakon jami'an tsaron filayen sauka da tashi na jirgin kasar gudu daga cikin kasar, don haka ne aka ba wa kamfanin haramtacciyar kasar Isra'ilan kwangilar tabbatar da tsaro a cikin su.

Tags

Ra'ayi