Apr 19, 2018 18:03 UTC
  • Jiragen Yakin Iraki Sun Kai Hare-Hare Sansanonin 'Yan ISIS A Siriya

Gwamanatin kasar Iraki ta sanar da cewa sojin saman sun kaddamar da wasu munanan hare-hare kan sansanonin 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Daesh da suke cikin kasar Siriya a kokarin da kasahen biyu suke yi na ganin bayan wannan kungiyar ta ta'addanci a kasashen biyu.

A wata sanarwa da ya fitar a yau din nan Alhamis, ofishin firayi ministan kasar Irakin  Haider al-Abadi ya bayyana cewar sojojin kasar sun kaddamar da wasu hare-hare ta sama kan sansanonin 'yan kungiyar ta Daesh a cikin kasar Siriya.

Sanarwar ta ce firayi minista Al-Abadi ne ya ba da umurnin kai wadannan hare-hare saboda hatsarin da 'yan ta'addanci suke da shi ga kasar Iraki da kuma barazanar da suke ci gaba da yi wa kasar.

Kakakin sojin kasar Irakin Birgediya Janar Yahya Rasool, ya ce an yi amfani da jiragen yakin samfurin F-16 ne wajen kai wadannan hare-haren bayan tattaunawa da mahukutan kasar Siriya da kuma sanar da su lamarin.

Duk da nasarar da kasashen biyu suka samu na fatattakan 'yan kungiyar Daesh din a kasashensu da kuma karya lagonsu, amma har ya zuwa yanzu akwai sauran gyauronsu  a kan iyakokin kasashen biyu.

 

Tags

Ra'ayi