• Harin Kunar Bakin Wake Ya Yi Ajalin Mutum A Kalla 31 A Afganistan

Hukumomin kiwan lafiya a Afganistan sun ce a kalla mutane 31 ne suka rasa rayukansu, kana wasu 54 na daban suka raunana, biyo bayan wani harin kunar bakin wake a kabul, babban birnin kasar.

Bayanan daga kasar sun ce an kai harin ne a wata cibiyar rejistar zabe dake unguwar Hazara ta galibi 'yan Shi'a a safiyar yau Lahadi.

Wannan harin dai ya tabbatar da barazanar rikicin da kasar ke fama da shi, gabanin zaben kasar na watan Oktoba mai zuwa.

Kungiyar Taliban mai dauke da makamai a kasar, ta musunta hannunta a harin.   

Tags

Apr 22, 2018 11:16 UTC
Ra'ayi