• Yahudawan Sahyuniya Sun Kai Samame A Gabashin Birnin Quds

Rahotanni daga Palastine sun cewa, Falastinawa da dama suka jikkata sakamakon auka musu da sojojin yahudawan Isra’ila suka yi a yankin Abu Dis da ke gabashin Quds.

Shafin yada labaran na Al-nashrah ya bayar da rahoton cewa, sojojin yahudawa gami da jami’an ‘yan sandan yahudawan Isra’ila, sun kutsa kai da safiyar yau a yankin Abu Dis, inda suka yi ta bincike a gidajen Falastinawa mazauna yankin, wanda hakan ya harzuka matasa suka shiga arangama da su.

Jami’an tsaron yahudawan sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye, wanda yake dauke da wasu sanadarai da ke shake dan adam, wanda hakan ya sanya Falastinawa da dama suka galabaita, wasu kuma suka samu raunuka.

Yankunan Falastinawa da ke gabashin birnin Quds dai sun saba ganin irin wannan cin zarafi daga jami’an tsaron Isra’ila, wanda hakan kan sanya matasa su dauki matakin yin ruwan duwatsu da kona tayoyi, da hakan kan sanya yahudawan ala tilas su ja da baya.

Apr 24, 2018 19:17 UTC
Ra'ayi