Mayu 19, 2018 05:31 UTC
  • MDD Ta Amince Da Binciken Zubar Da Jini A Gaza

Kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya, ya amince da kudirin aike wa da wata tawagar kasa da kasa ta kwararru masu binciken laifukan yaki a zirin Gaza.

Tawagar dai za ta yi bincike ne kan take hakkin bil adama da kuma cin zarafi a Zirin na Gaza, bayan kisan Palasdinawa sama da 60 da sojojin 'yan sahayoniya suka yi a ranar Litin data gabata.

Kasashe biyu ne dai da suka hada da Amurka da Austria suka nuna kin amincewa da kudirin, a yayin da kasashe 29 cikin 47 suka amince da shi, sai 14 wadanda suka hada da Switzerland da Jamus da kuma Biritaniya suka yi rawar kuri'arsu.

Kudirin da aka amince da shi ya bukaci aikewa cikin gaggawa da wani kwamitin koli na kasa da kasa mai zaman kansa, don gudanar da binciken ciki har da na laifukan yaki kan amfani da karfi na sojojin Isra'ila a zanga zanga da Palasdinawa ke yi tun ranar 30 ga watan 2018.

Saidai Isra'ila da Amurka sun yi tir da amunce wa da matakin kwamitin kare hakkin bil adama na MDD, wanda suka danganta dana makirci da kuma cewa mafi akasarin mambobinsa masu kyammar Isra'ila ne.  

 

Tags

Ra'ayi