Mayu 24, 2018 06:28 UTC
  • Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa Ta Maida Martani Kan Kasar Guatemala

Kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta sanar da kawo karshen duk wata alaka tsakaninta da kasar Guatemala sakamakon matakin da gwamnatin kasar ta dauka na maida ofishin jakadancinta zuwa birnin Qudus.

Kakakin kungiyar hadin kan kasashen Larabawa Mahmud Afifi ya sanar da cewa: Kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta kawo karshen duk wata yarjejeniyar fahimtar juna da ta kulla da gwamnatin Guatemala sakamakon matakin da mahukuntan kasar suka dauka na bin sahun kasar Amurka wajen maida ofishin jakadancinsu zuwa birnin Qudus daga Tel-Aviv.

A ranar Laraba 16 ga wannan wata na Mayu ne gwamnatin kasar Guatemala ta bi sahun kasar Amurka wajen maida ofishin jakadancinta daga Tel-Aviv zuwa birnin Qudus. Tun a ranar Litinin 14 ga wannan wata na Mayu ne gwamnatin Amurka ta maida ofishin jakadancinta zuwa birnin na Qudus mallakin Palasdinawa lamarin da ya janyo boren Palasdinawa ta hanyar gudanar da zanga-zangar lumana amma sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka bude musu wuta da ya janyo shahadar Palasdinawa fiye da 60 tare da jikkatan wasu kimanin 3000 na daban.

Tags

Ra'ayi