Jun 03, 2018 05:51 UTC
  • Gaza : An Yi Jana'izar 'Yar Agajin Da Sojojin Mamaya Suka Kashe

A Palasdinu, dubban mutane ne suka halarci jana'izar 'yar agajin nan da sojojin mamaya na Isra'ila suka kashe t aharbin bindiga a kusa da iyaka da zirin Gaza.

Rahotannin daga yankin, sun ce an samu Palasdinawa da dama da suka raunana a wata arangama tsakanin sojojin yahudawan da kuma harba rokoki a kudancin Isra'ila bayan jana'izar.

A ranar Juma'a data gabata ne, matashiyar 'yar Palasdinu mai suna, Razan al-Najjar, 'yar shekara 21, ta rasa ranta sanadin raunin harbin bindiga na sojojin Isra'ilar 'yan kama wuri zauna. 

A cewar kakakin ma'aikatar lafiya na yankin Gaza, Achraf al-Qodra, 'yar agajin dake aikin sa kai, na sanye da fararen tufafi na ma'aikatan lafiya.

Rasuwar, matashiyar 'yar agajin, ya sanya adadin Palasdinawa da sukayi shahada ta harbin bindigan sojojin yahudawan mamaya na Isra'ila , zuwa 123, tun bayan boren da Palasdinawan ke yi na kwato hakkokinsu.

Tags

Ra'ayi