• Dakarun Yamen Sun Mayar Da Martani Da Makami Mai Linzami Kan Saudiyya

Dakarun kasar Yemen tare da mayakan sa kai na kabilun larabawan kasar sun mayar da martaniya da jijjifin safiyar yau a kan wani babban sansanin sojin gwamnatin Saudiyya a kudancin kasar.

Shafin tashar talabijin na Almasirah ya bayar da rahoton cewa, a safiyar yau dakarun kasar Yemen tare da mayakan sa kai na kabilun larabawan kasar sun harba makami mai linzami a kan sansanin sojin Al saud da ke gundumar Asir a kudancin kasar ta saudiyya.

Rahoton ya ce wannan yana zuwa ne biyo bayan hare-haren da jiragen yakin masarautar Saudiyya suka kaddamar ne a jiya Juma'a a kan biranen Sa'adah da Hudaidah, inda suka kashe fararen hula tare da rusa gidajen jama'a da kuma kaddarori masu tarin yawa.

Kasar saudiyya tare da taimakon Aurka da Isra'ila gami da Birtaniya, ta kwashe tsawon shekaru ffiye da uku tana kaddamar da munanan hare-hare a kan kasar Yemen da sunan yaki da kungiyar Alhuthi da ba su dasawa da ita, inda wadannan hare-hare ya zuwa yanzu suka yi sanadiyyar mutuwar dubban fararen hula da suka hada da mata da kananan yara, tare da rusa daruruwan masallatai, makarantu asibotoci cibiyoyin kasuwanci da sauransu.

Tags

Jun 23, 2018 09:13 UTC
Ra'ayi