Jul 12, 2018 15:09 UTC
  • Sojojin Siriya Sun Karbe Ikon Birnin Deraa

Rahotanni daga Siriya, na cewa sojojin kasar sun samu kutsawa cikin birnin Deraa, inda sukayi nasara karbe daukacin birnin daga hannun gungun 'yan adawa dake dauke da makamai.

Wannan dai na zuwa ne bayan da sojojin suka tsarkake lardunan da gabashi da kuma yammaci na lardin Deraa.

Gidan talabijin na Al-Mayadeen ya raiwato wani labarin gaggawa dake cewa, sojojin Siriya da masu mara masu baya sun kai ga karbe daukacin ikon birnin na Deraa, dake kudancin kasar ta Siriya.

Birnin Deraa wanda nan ne aka fara doren adawa da gwamnatin Bashar Al Assad, ya kwashe shekaru da dama a hannun gungun mayakan 'yan adawa masu dauke da makamai a yankin kudu maso yammacin Siriyar.

Tags

Ra'ayi