Jul 12, 2018 16:07 UTC
  • Amnesty Int. Ta Zargi UAE Da Aikata Laifukan Yaki A Yemen

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa, Amnesty International, ta zargi Hadaddiyar Daular Larabawa da aikata laifukan yaki a kasar Yemen.

Hadaddiyar Daular Larabawa dai ita ce babbar kawa ga Saudiyya dake jagorantar yaki a Yemen tun cikin watan Maris na shekara 2015 data gabata.

A rahoton data fitar Amnesty, ta zargi Hadaddiyar daular larabawa, da cin zarafi, takura wa, fyade a wasu gidajen yari na kasar ta Yemen.

Rahoton da Amnesty ta fitar a yau Alhamis ya kuma ambato cewa akwai mazaje da dama wadanda aka batar dasu da karfi tsiya, bayan cafkesu ba bisa ka'ida ba, wanda hakan ya sabawa 'yancin dan adam, kuma tamakar laifukan yaki ne.

Amnesty International, ta ce kawai ana fakewa da yaki da ta'addanci don cafke 'yan adawa.

A nata bangare dai Hadaddiyar Daular Larabawar ta musanta duk wadanan zarge zargen musamman na cewa tana rike da ikon wasu gidanjen yari a boye a kudancin kasar ta Yemen.

Tags

Ra'ayi