• Shugaban Kungiyar Ansarullah Ya Ce Yana Iya Amincewa Da Sanya Idon MDD A Hudaida Amma Da Sharadi

Shugaban kungiyar Ansuraullah ta kasar Yemen Abdul-Malik Badruddin Huthi ya bayyan cewa ba zai ki bukatar MDD ta sanya ido a kan lamuran da ke faruwa a birnin Hudaida na bakin ruwa ba amma da sharadin kawancin kasashen da suke yakarsa kasar su dakatar da hare haren da suke kaiwa a kan birnin na Hudaida.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa shugaban na Ansarallah ya bayyana haka ne a hirar da ta hada shi da jaridar Le Figaro ta kasar Faransa. Ya kuma kara da cewa kafin haka ya fadawa jakadan majalisar dinkin duniya na warware rikicin kasar Yeman Martin Griffiths kan cewa dole ne kasashen saudia da kawayenta su dakatar da kai hare haren kan birnin Hudaida kafin su kyale jami'an MDD su shiga birnin.

A ranar 13 ga watan Yunin da ya gabata ce mayakan saudia da na tsohon shugaban kasar Abdu Rabbu Mansur Hadi suka farwa birnin Hudaida ya yaki da nufin kwatarsa daga hannun mayakan gwamnatin kasar Yeman amma sun kasa yin hakan don tsananin turjiyan da suka gamu da ita daga mayakan nan Huthi. Saudia tana ganin mayakan na huthi suna amfani da birnin na bakin ruwa don shigo da makamai.

 

Tags

Jul 18, 2018 12:08 UTC
Ra'ayi