Aug 13, 2018 12:48 UTC
  • Kungiyar Hamas Ta Gargadi Isra'ila Akan Ci Gaba Da Yi Wa Gaza Barazana

Reshen soja na kungiyar ta Hamas, ya fitar da wani bayani wanda a ciki ya yi gargadin cewa dun wani wuce gona da iri da 'yan sahayoniya za su yi a Gaza zai fuskanci mayar da martani

Hassam Badran wanda jami'i ne a kungiyar ta Hamas ya bayyana cewa; Barazanar kashe jagororin Hamas da 'yan Sahayoniya su ka yi ba sabo ba ne, kuma abin dariya ne domin hatta yaran palasdinawa ba su tsoron irin wannan barazanar.

Hassam Badran ya ci gaba da cewa; Lokacin da 'yan sahayoniya za su tafka laifi su sha ya wuce.

Jaridar Haaretz ta 'yan sahayoniya ta buga labarin da ke cewa; Jami'an leken asirin Sahayoniya sun shirya da tsara kai hari domin kashe jagororin Hamas

Tags

Ra'ayi