Aug 22, 2018 06:25 UTC
  • Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa Ta Bukaci Daukan Matakin Kalubalantar Bakar Siyasar H.K.Isra'ila

Kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta Arab League ta bukaci hanzarta daukan matakin kalubalantar bakar siyasar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kan Masallacin Aksa da ke birnin Qudus.

A jawabinsa a jiya Talata dangane da juyayin cikar shekaru arba'in da tara da kona wani bangaren Masallacin Aksa da tsagerun Yahudawan Sahayoniyya suka yi a wancan lokacin: Mataimakin babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen Larabawa kan harkokin da suka shafi al'ummar Palasdinu Sa'id Abu-Ali ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta hanzarta tsoma baki wajen ganin an hana gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila canza tsarin gine-ginen Masallacin Aksa mai tsawon tarihi.

Har ila yau Sa'id Abu-Ali ya fayyace cewa: Kusan a kullum rana sai tsagerun yahudawan sahayoniyya sun dauki matakin keta hurumin Masallacin Aksa lamarin da ke bukatar daukan matakin hana ci gaba da faruwan irin wannan rashin mutunci.

Tags

Ra'ayi