Aug 22, 2018 18:53 UTC
  • Sojojin Yemen Sun Kwace Iko Da  Sansanonin Soja A Yammacin kasar

Majiyar tsaron kasar Yemen ta ce sojoji da dakarun sa kai na Ansarullah sun kame yankuna da dama da su ke a yammacin kasar

Tashar talabijin din al-alam mai watsa shirye-shieyenta daga nan Iran ta ce; Sojojin na Yemen da kuma dakarun sa kai na Ansarullah sun kai gaggaurmin hari wanda ya kare da korar 'yan koren Saudiyya daga garin Hays da ke yankin Hudaidah

Rahoton ya ci gaba da cewa; Da dama daga cikin 'yan koren Saudiyyar sun rasa rayukansu yayin da wasu su ka jikkata.

Tashar ruwa ta al-Haudaidah ce babbar cibiyar da ake shigar da kayan agaji cikin kasar Yemen daga waje. Saudiyya da kawayenta bisa cikakken goyon bayan Amurka da taimakonta, ta fara kai hari a Yemen a 2015, wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci dubban rayuka.

Tags

Ra'ayi