Aug 24, 2018 12:56 UTC
  • Amnesty TA Yi Kira Ga Saudiyya Da Ta Soke Hukuncin Kisan Da Wasu Masu Fafutuka

Kungiyar kare hakkin Dan'adam din tana son ganin mahukunta a Saudiyyar ba su kashe Isra, algamgam da wasu mutane hudu da suke tare da ita ba

Shugaban kungiyar kare hakkin dan'adam a yankin gabas ta tsakiya Samah Hadid ya ce; Aiwatar da hukuncin kasan akan wadannan 'yan fararen hular zai kuma jefa rayuwar suaran masu rajin kare hakkin dan'adam da ake tsare da su cikin hatsari.

Hadid ya ce manufar hukunta al-gamgam, shi ne rufe bakunan sauran masu rajin kare hakkin bil'adama a cikink kasar ta Saudiyya wanda hakan yana cikin karo da dokokin kasa da kasa.

Al-gamgam wacce yar shekaru 29 ne jami'an tsaron Saudiyyar sun kama ta a tare da maigidanta Musa al-Hashim a 2015m saboda sun yi Zanga-zanga a yankin Katif da ke gabacin kasar.

A cikin shekarn bayan nan jami'an tsaron Saudiyya sun rika kama masu rajin kare hakkin dan'adam da malaman addini wadanda suke yin suka ga gwamnati

Tags

Ra'ayi