Sep 01, 2018 06:31 UTC
  • Amurka Ta Yanke Dukkan Tallafin Da Take Bawa Palasdiwa Yan Gudun Hijira

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta bada sanarwan dakatar da tallafin kudade da ta saba bawa yan gudun hijira Palasdinawa karkashin kungiyar nan ta UNRWA.

Kamfanin dillancin labaran Farsnews na kasar Iran ya nakalto ma'aikatar tana fadar haka a jiya Jumma'a ta kuma kara da cewa daga yanzu gwamnatin Amurka ba zata bawa Palasdinawa yan gudun hijira kudaden da ta saba ba. Banda haka a ranar 24 ga watan Augustan da ya gabata gwamnatin Amurkan ta ce ta dakatar da biyan Dalar Amurka miliyon 200 ga yankin Gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan da ta saba yi.

Gwamnatin Amurka ta dauki wannan matakin ne don tilastawa Palasdinawa amince da wani shirin da ta kira shia "Sulhuntawan Karni ". Sulhuntawa wacce ta bukaci Palasdinawa su yi bankwana na birnin Qudus don na yahudawa ne, sannan sauran Palasdinawa da suke gudun hijira a cikin kasarsu da aka mamaye ko a sauran kasashen duniya basa da incin dawowa gida kuma sun tafi ne har abada. 

Har'ila yau sulhuntawan karni ta takaida kasar Palasdina a yankin gaza da yankin yamma da kogin Jordan kadai. 

Tags

Ra'ayi