Sep 03, 2018 19:00 UTC
  • Kungiyar Agajin Palasdinawa

Kakakin Kungiyar Agajin ta Unruwa Chris Gunness ya ce; Palasdinawa miliyan 4.5 za su cutu daga yanke taimakon kudaden da Amurka ta yi.

Kakakin "Unruwa" ya ci gaba da cewa; Matakin da Amurkan ta dauka yana cin karo da kudurin Majalisar Dinkin Duniya, kuma dubban palasdinawa da su ka hada da kananan yara ne za su cutu.

Gunness ya yi kira ga sauran kasashen duniya da su cike gibin da janyewar Amurka ta haifar ta fuskar kudaden taimako.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ce ta sanar da yanke taimakon kudaden da take bai wa kungiyar ta Unruwa wacce aka kafa ta da kudurin Majalisar Dinkin Duniya.

Da akwai palasdinawa miliyan biyar da rayuwarsu take damfare da taimakon da suke samu daga kungiyar Unruwa.

Tags

Ra'ayi