Sep 04, 2018 06:34 UTC
  • Amurka Ta Gargadi Kasashen Rasha Da Iran Kan Harin Da Suke Son Kaiwa Yan Ta'adda A Idlib

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya gargadi kasashen Rasha da Iran kan anniyarsu ta tallafawa gwamnatin kasar Siriya ta kwace tungar yan ta'adda na karshe a kasar wato garin Idlib.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana bayyana haka ne a shafinsa na Tweeter, inda ya kara da cewa kaiwa birnin Idlib hari zai jawo mutuwar dubban mutane. Banda haka Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo da kuma jakadan kasar a MDD Nikki Haley duk sun yi irin wannan maganar. 

Gwamnatocin kasashen Rasha da Iran ne suka tallafawa sojojin kasar Siriya suka kwace mafi yawan kasar Siriya daga hannun yan ta'adda a cikin shekaru kimani 7 da suka gabata. 

Garin idlib shi ne tungar yan ta'addan ta karshe a kasar Siria. A halin yanzu dai sojojin kasar syria suna jirin umurnin gwamnatin kasar ne kawai kafin su fara yakin dawo da ikon gwamnati a birnin na Idlib.

 

Tags

Ra'ayi