Sep 04, 2018 18:14 UTC
  • Masar: Wani Bom Ya Tashi A Kusa Da Ofishin Jakadancin Amurka

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambato cewa bom din ya fashe ne akan titin Simon Bolivar da ke birnin al-kahira, inda nan ne ofishin jakadancin Amurka yake.

Wata majiyar tsaron Masar ta ce an kama wani mutum guda wanda ake zaton cewa shi ne ya jefa bom din na kwalba. Sai dai majiyar ta ce babu wani lahani da bom din ya haddasa.

Ofishin jakadancin Amurka a kasar ta Masar ya ce yanzu haka ya fara gudanar da bincike domin gano bakin zaren abin da ya faru. Bayanin ya kuma kira yi Amurkawa mazauna kasar ta Masar da su kasance cikin fadaka.

Kawo ya zuwa yanzu babu wani bangare da ya dauki alhakin kai harin ko kuma dalilinsa.

Jaridar al-misriyyun ta buga a shafinta cewa; An yi musayar wuta a tsakanin 'yan sanda da kuma wasu mutane masu dauke da makamai a yankin al-ayn al-shukhnah, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 4.

Tags

Ra'ayi