Sep 04, 2018 18:16 UTC
  • Syria: Amurka Tana Bai Wa

Ma'aikatar harkokin wajen Syria ta fitar da bayani da a ciki ta bayyana cewa; Amurka da kawayenta suna ba da makamai ga 'yan ta'addar kungiyar Nusrah da kuma Da'esh

Bayanin ya ci gaba da cewa; Ta hanyar wata kasa mai shiga tsakani, musamman daga gabacin turai, Amurkan take aike wa da 'yan ta'addar kungiyoyin Nusrah da Da'esh makamai da sauran kayan yaki.

A wani labarin daga Syria, sojojin kasar sun halaka 'yan ta'adda 50 a yankin Afrin.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Right Watch ta ce da akwai wasu manyan kwamandojin 'yan ta'adda biyu a tsakanin wadanda aka kashen.

A cikin kwanakin sojojin Syria suna jan damarar yaki domin 'yanto da yanki na karshe da ke hannun 'yan ta'adda, wato yankin Idlib.

 

Tags

Ra'ayi