Sep 05, 2018 11:50 UTC
  • Palasdinawa 25 Sun Jikkara A kan Iyaka Da Yankin Gaza

Majiyar Palasdinawa ta ambaci cewa; sojojin Sahayoniya sun bude wuta akan masu Zanga-zangar akan iyaka da yankin na Gaza

A yau Laraba kamfanin dillancin labarun Mehr ya nakalto cewa; Palasdinawan suna ci gaba da gudanar da Zanga-zangar da suke yi ne akan hakkinsu na komawa yankunansu da aka kore su daga ciki, a yayin da aka bude musu wutar.

Bugu da kari masu Zanga-zangar sun yi Allah wadai da matakin da Amurka ta dauka na yanke taimakon kudaden da take bai wa kungiya mai ba da agaji ga palasdinawa 'yan gudun hijira, wato Unruwa.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yanke tallafin da take bai wa Unruwa ne a ranar 31 ga watan Agusta da ya kare.

An kafa hukumar Unruwa ne tun a 1949, kuma da akwai palasdinawa fiye da miliyan 5 da rayuwarsu take damfare da taimakon da suke samu daga gare ta.

Tags

Ra'ayi