Sep 06, 2018 08:23 UTC
  • Dakarun Yemen Sun Halba Makamai Masu Linzami Zuwa Kudancin Saudiya

Dakarun tsaro da mayakan sa kai na kasar yemen sun halba makamai masu linzami kan sansanin dakarun tsaron Saudiya a lardin Najran na kudancin kasar a daren jiya laraba

Kamfanin dillancin labaran Fars ya habarta cewa Dakarun tsaro da mayakan sa kai na kasar yemen sun halba makami mai linzami samfarin Badar na 1 kan sansanin dakarun saudiya a lardin Najran dake kudancin kasar, kuma ya zuwa yanzu ba a bayyana irin hasarar da wannan hari ya janyo ba.

A daren talatar da ta gabata ma, Dakarun tsaro da mayakan sa kai na kasar yemen din sun harba makami mai linzami samfarin Badar na 1 kan matatar Man fetir da kamfanin Petro chimie na kamfanin man kasar Saudiya ARAMCO dake yankin Jizan na kusancin Saudiya.

Kakakin Dakarun tsaron Yemen Sharaf Lukuman ya tabbatar da ci gaba da kai farmaki kan ma'aikatu da cibiyoyin tattalin arzikin saudiya hr lokacin da mahukunta Al-sa'oud din za su kawo karshen kai hare-hare da kuma killace kasar ta yemen.

Duk da irin killacewar da kawancen Saudiya ya yiwa kasar ta Yemen, karfin kariya da tsaron kasar na kara karuwa.

Tags

Ra'ayi