Sep 06, 2018 11:49 UTC
  • Buhari Ya Bukaci Tallafin China Domin Ci Gaban Tattalin Arzikin Najeriya

Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyanawa takwaransa na kasar China Xi Jinping kan cewa gwamnatinsa ta na matukar son ganin an kammala aikin gina madatsar ruwa mai bada wutan lantar a yankin Mambila na jihar Taraba.

Tashar talabijin ta channelstv ta nakalto shugaban yana fadar haka ne a ganawarsa da takwaransa na kasar China a jiya Laraba a birnin Bejin babban birnin kasar China. 

Buhari ya bukaci tallafin kasar China don ganin an kammala wannan gagarumin aikin wanda ake saran idan an kammala shi zai samar da wutan lantarki mai karfin Magawats 3050. 

Shekara guda da ta gabata kenan gwamnatin Najeriya ta amince da fara aikin gina madatsar ruwan ta Mambila wacce zata lakume dalar Amurka Biliyon 5.797. Manitan makamashi, ayyuka da kuma gidaje babatunde Fashola ya bayyana cewa aiki zai dauki watanni 72 kafin a kammala shi. Sannan gwamnatin Najeriya ce zata biya kashi 15 na wadannan kudade a yayin da gwamnatin kasar China zata biya sauran a matsayin bashi

 

Tags

Ra'ayi