Sep 06, 2018 16:41 UTC
  • Nasrallah: Amurka da 'Isra'ila' Sun Gaza Wajen Cimma Manufarsu A Gabas Ta Tsakiya

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, Sayyid Hasan Nasrallah, ya bayyana cewar Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila sun sha kashi cikin dukkanin makirce-makircen da suka kulla don cimma bakar aniyarsu a yankin Gabas ta tsakiya.

Kafafen watsa labarai sun jiyo shugaban kungiyar ta Hizbullah yana fadin hakan inda ya ce Amurka da kawayenta sun yi iyakacin kokarinsu wajen haifar da rashin tabbas a yankin Gabas ta tsakiya ciki kuwa har da kasashen Yemen, Iraki, Siriya da kuma Labanon duk dai don cimma bakar aniyarsu ciki kuwa har da ganin bayan 'yan Shia.

Sayyid Nasrallah ya ce Amurka da kawayen na ta sun kirkiro kungiyoyin ta'addanci na takfiriyya don zubar da jinin 'yan Shi'a a kasashe daban-daban, yana mai kafa misali da yakin da Saudiyya ta kaddamar a kan al'ummar kasar Yemen bisa goyon bayan Amurka.

A wani bangare na jawabin nasa, shugaban kungiyar ta Hizbullah ya ce sakamakon kashin da Amurka, Isra'ila da kawayen nasu musamman Saudiyya suka fuskanta, yanzu kuma suna ta kokari wajen mai da irin wannan yakin kan kasar Iran ta hanyar sanya mata takunkumi da nufin karya tattalin arzikin kasar.

 

Tags

Ra'ayi