Sep 07, 2018 05:40 UTC
  • Iraki: An Harba Makaman Roka Akan Babban Cibiyar Gwamnatin Iraki A Bagadaza

Rahotanni da suke fitowa daga Irakin sun ce an harba makaman roka din ne dai akan cibiyar da ake kira da; Green Zone' da ke cikin birnin bagadaza a jiya alhamis

Yankin dai yana dauke da cibiyoyin gwamnatin Iraki, haka nan ofisoshin jakadancin kasarshen waje.

A cikin shekaru biyu na bayan nan wannan shi ne karon farko da aka kai hari irin wannan a Irakin.

A cikin kwanakin bayan nan Iraki tana cike da dambaruwar siyasa inda jam'iyyun kasar su ka kasu gida biyu, kowane bangare na ikirarin yana da kawancen 'yan majlisa mafi girma, da zai ba shi damar kafa gwamnati.

A gefe daya al'ummar garin Basara suna ci gaba da Zanga-zanga domin nuna rashin jin dadinsu akan karancin kayan bukata na rayuwa da suka hada wutar lantark da ruwan sha.

A jiya asabar ma wasu daga cikin masu Zanga-zanga sun cinna wuta akan ofishin gwamnan yankin na Basra.

Ra'ayi