Sep 08, 2018 18:52 UTC
  • Jiragen Saman Yakin Rundunar Kawancen Saudiyya Sun Kashe Mutane A Lardin Ma'arib Na Yamen

Jiragen saman yakin rundunar kawancen Saudiyya sun yi luguden wuta a kan lardin Ma'arib da ke kasar Yamen, inda suka kashe mutane biyar kuma uku daga cikinsu mata.

Tashar talabijin ta Al-Masirah ta kasar Yamen ta watsa rahoton cewa: Jiragen saman yakin rundunar kawancen Saudiyya sun kai wasu jerin hare-haren wuce gona da iri kan yankunan Atlas da Sahraw da suke lardin Ma'arib a jiya Juma'a, inda suka kashe mutane biyar kuma uku daga cikinsu mata.

A gefe guda kuma sojojin Yamen da hadin gwiwar dakarun sa-kai na kasar sun harba makamai masu linzami kan sansanin sojojin hayar Saudiyya da ke yankin Karsh a lardin Lahij na kasar ta Yamen, inda suka janyo hasarar rayuka tare da jikkata sojojin hayar.  

Ra'ayi