Sep 09, 2018 07:31 UTC
  • An Hallaka Wasu Sojojin Saudiyya, Da Wasu Sojojin Hayarta A Kasar Yemen

Rahotanni daga kasar Yemen sun bayyana cewar wasu sojojin Saudiyya tare da wasu sojojin haya masu goya wa korarren shugaban kasar Yemen din Abd Rabbuh Mansur hadi sun hallaka biyo bayan wani hari da sojojin kasar ta Yemen da suke samun daukin sojojin sa kai na kasar suka kai sansanoninsu da ke kan iyakar kasashen biyu.

Kafar watsa labaran Saba News ta kasar Yemen din ta jiyo wata majiya sojin kasar tana cewa sojojin Yemen din sun harba makami mai linzami samfurin Badr-1 kan wani taron na sojojin Saudiyya a yankin Asir da ke kan iyakar kasashen biyu lamarin da yayi sanadiyyar hallaka wasu da kuma raunana wasu da dama.

Har ila yau labarin ya kara da cewa a wani harin na daban kuma da dakarun na Yemen suka kai wani sansanin sojojin haya na Saudiyyan da ke yankin al-Arab, sun sami nasarar hallaka wasu sojojin hayan su 8, kamar yadda wasu rahotannin kuma sun ce dakarun na Yemen sun kai wasu hare-haren sansanonin sojin Saudiyya din da ke yankin Al-Sharafa na lardin Najran inda a nan ma an hallaka wani sojan na Saudiyya.

Dakarun na Yemen dai suna kai wadannan hare-hare ne a matsayin mayar da martani ga hare-haren wuce gona da iri da Saudiyya da kawayenta suke ci gaba da kai wa kasar lamarin da ke ci gaba da zubar da jinin al'ummar kasar.

 

Tags

Ra'ayi