Sep 09, 2018 11:50 UTC
  • Daya Daga Cikin Jagororin Kungiyar Ta'addanci Ta Jubhatun-Nusrah Ya Nemi Mafaka A Turkiyya

Majiyar gwamnatin Siriya ta sanar da cewa: Daya daga cikin jagororin kungiyar ta'addanci ta Jubhatun-Nusrah da suke da hannu a harhada makamai masu guba a kasar Siriya ya nemi mafaka a kasar Turkiyya.

Tashar talabijin ta Al-Mayadeen da ke kasar Lebanon ta watsa rahoton cewa: Gwamnatin Siriya ta sanar da cewa daya daga cikin manyan jagororin kungiyar ta'addanci ta Jubhatun-Nusrah kuma masanin harhada makamai masu guba ya tsere cikin kasar Turkiyya daga kasar Siriya yana neman mafaka a can.

Majiyar gwamnatin Siriya ta kara da cewa: Bayan fatattakan 'yan ta'adda daga kauyen Jusurul-Shughur da ke lardinb Idlib an gano tarin makamai masu guba a maboyar kungiyar ta'addanci ta Jubhatun-Nusrah.

A halin yanzu haka dai sojojin gwamnatin Siriya da dakarun sa-kai da suke tallafa musu sun samu nasarar tsarkake yankunan kasar daga 'yan ta'adda, kawai saura wasu yankunan lardin Idlib ne suke hannun gungun 'yan ta'adda kuma ya zuwa yanzu sun fara tserewa daga yankunan, inda wasu suke tsallakawa zuwa cikin kasar Turkiyya.   

Tags

Ra'ayi