Sep 12, 2018 07:03 UTC
  • Jiragen Saman Yakin Saudiyya Sun Kashe Mutane Uku Iyalan Gida Guda A Kasar Yamen

Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya suna ci gaba da yin luguden wuta kan yankunan kasar Yamen tare da kashe fararen hula da suka hada da mata da kananan yara.

Tashar Al-Masirah ta kasar Yamen ta watsa rahoton cewa: Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun kai wasu jerin hare-hare kan yankin Al-Jabaliyyah da ke lardin Hudaidah a kudancin kasar Yamen, inda suka kashe mutane uku iyalan gida guda tare da jikkata wani mutum guda na daban.

Har ila yau Khalid Assha'if babban diraktan filin jirgin saman kasa da kasa da ke birnin Sana'a fadar mulkin kasar Yamen ya koka kan yadda mahukuntan Saudiyya suka dauki matakin hana tashin jiragen sama daga birnin na Sana'a domin jigilar marassa lafiya zuwa kasashen waje da nufin yi musu jinya sakamakon nau'o'in rashin lafiya ko jikkata da suka samu sanadiyyar hare-haren wuce gona da irin rundunar kawancen Saudiyya kan fararen hulan kasar lamarin da ke matsayin take hakkin bil-Adama karara.

Ra'ayi