Sep 12, 2018 07:24 UTC
  • Kungiyar Arab League Ta Yi Allah Wadai Da Rufe Ofishin Kungiyar 'Yanto Palasdinu Ta PLO A Amurka

Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ya yi Allah wadai da rufe ofishin kungiyar 'yanto Palasdinu da ke birnin Washington na kasar Amurka.

A bayanin da babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta Arab League Ahmed Abu-Gheit ya fitar a jiya Talata ya yi Allah wadai da matakin rufe ofishin kungiyar 'yanto Palasdinu ta PLO da ke birnin Washington na kasar Amurka tare da bayyana matakin da cewa: Daya ce daga cikin bakar siyasar Amurka kan al'ummar Palasdinu.

Bayanin ya kara da cewa: Tun daga lokacin da gwamnatin Amurka ta sanar da birnin Qudus a matsayin fadar mulkin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila tare da aniyarta ta maida ofishin jakadancinta daga Tel-Aviv zuwa birnin na Qudus, ya bayyana a fili cewa gwamnatin Amurka tana goyon bayan ayyukan ta'addanci da wuce gona da irin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ido rufe. 

Tags

Ra'ayi