• Ma'aikatar Tsaron Rasha Ta Dora Alhakin Harbo Jirginta A Syria Akan Haramtacciyar Kasar Isra'ila

A wata sanarwa da ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta fitar a dazu, ta ce jiragen yakin Isra'ila sun yi garguwa da jirgin Saman Rasha da aka harbo

Kamfanin dillancin labaran Sputnic ya ambato ma'aikatar tsaron kasar ta Rasha tana nuna taswirar hanyar da jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila samfurin F-16 suke bi a samaniyar Laizkiyya na syria, da kuma hanyar da jirgin Rasha Ilushin 20 yake bi, abin da yake nuni da garkuwar da jiragen yakin Isra'ila su ka yi da shi.

Rahoton ya kuma bayyana yadda jiagen yakin na Haramtacciyar kasar Isra'ila suke bibiyar jirgin soja na Ilyushin da yake kan hanyarsa ta zuwa sansanin sojan Rasha na Hamimin a gundumar Lazikiyya.

Ministan tsaron kasar Rasha Sergey Choigou ya dora alhakin harbo jirgin da kashe sojoji 15 da suke cikinsa akan wuyan haramtacciyar kasar Isra'ila.

 

Tags

Sep 18, 2018 18:53 UTC
Ra'ayi