• Fiye Da Yara Miliyan 5 Ke Fuskantar Barazanar Yunwa A Yemen

Kungiyar tallafawa yara ta Save the Children ta ce fiye da yara miliyan biyar ne ke fuskantar barazanar yunwa a daidai lokacin da rikicin kasar ke kara kamari kuma farashin kayan abinci ya yi tashin gwaron zabo.

A rahoton data fiyar yau kungiyar ta yi gargadi akan iya fusknatar matsanaciyar yunwa wacce babu kamarta a wannan kasar dake fama halin jin kai mafi muni a duniya. 

Sace tahe Children ta yi kiyasin cewa akwai karin yara miliyan guda dake cikin hadarin yunwa a daidai lokacin da farashin kayan abinci ke dada karuwa, wanda ya kai ga adadin yaran dake fuskanatr barazanar yunwa ya kai miliyan 5,2 a wannan kasar ta Yemen.

A wani labari kuma Hukumar kula da abinci ta MDD,  ta ce lokaci na kara kurewa, a kokarin shawo kan fadawa yunwa mafi muni a kasar, a don haka ba zata lamunta da duk wani abu da zai kawo mata tsaiko a cikin shirinta na raba kayan agaji ba..

Tun a watan Maris na 2015 da Saudiyya ta abkawa kasar ta Yemen da yaki, kimanin mutane 10,000 ne galibi fararen hula suka rasa rayukansu, kana wasu sama da 56,000 suka raunana, kuma a halin da ake ciki 'yan Yemen ukku cikin hudu ne ke bukatar agaji musamman na abinci, a daidai lokacin da kuma kasar ke fama da cutar amai da gudawa.

Tags

Sep 19, 2018 17:05 UTC
Ra'ayi