• Karbala: Miliyoyin Musulmi Na Gudanar Da Tarukan Ashura A Hubbaren Imam Hussain (AS)

Miliyoyin mabiya mazhabar shi'ar ahlul bait (AS) ne suke gudnar da tarukan juyayin shahadar Imam Hussain (AS) a yau hubbarensa da ke birnin Karbala na kasar Iraki a yau.

Kamfain dillancin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa, miliyoyin musulmi mabiya mazhabar ahlul bait (AS) da ma 'yan sunna da dama duk suna halarta wannan wuri a yau, inda ake juayayin shahadar jikan manzon Allah Imam Hussain (AS) da kuma sauran iyalan gidan manzon Allah da aka yi kisan gilla a wannan wuria  daidai irin wannan rana.

Tuna  cikin 'yan kwanakin ad suka gabata ne dai miliyoyin jama'a suka fara isa birnin daga ciki da wajen kasar Iraki, domin halartar wadannan taruka na tunawa da juyayin Ashura a Karbala.

A nasu bangaren mahukuntan kasar Iraki sun ce kimanin jami'an tsaro dubu 30 a cikin kayan sarki suke gudanar da ayyukan tabbatar da tsaro da kuma bayar da kariya ga masu gudanar da tarukan, sakamakon barazanar da ka fuskanta a lokutan baya daga 'yan ta'adda masu dauke da akidar kafirtya musulmi.

Tags

Sep 20, 2018 12:52 UTC
Ra'ayi