Sep 21, 2018 06:37 UTC
  • Shugaban Kungiyar Ansarullah: Al'ummar Yemen Ba Za Su Meka Wuya Ga Makiya Ba

Abdulmalik Badruddin al-Huthy Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen wanda ya gabatar da jawabi jiya alhamis a Sana'a babban birnin kasar Yemen ya tabbatar da cewa duk da irin kisa da ta'addancin da kawancen saudiya ke yi a kasar ba zai sanya al'ummar kasar ta meka wuya ba.

Sayyid Abdulmalik Badruddin al-Huthy ya tabbatar da goyon bayansa ga masu gwagwarmayar 'yanto kasar daga mamayar 'yan korar Amurka, sannan ya bukaci al'ummar yemen  su kasance a fagen daga na yammacin kasar domin kalubalanta makiya.

 Abdulmalik Badruddin al-Huthy har ila yau ya bayyana cewa kalubalantar mamayar makiya 'yan korar Amurka da kuma yaki da 'yan mamayar birnin Qudus a matsayin abi mai mahimancin gaske.

A nasa bangare Allama Shamsuddin Sharafuddin babban mai bayar da fatawa na kasar Yemen ya ce wajibi ne kalubalantar makiya da 'yan mamayar kasar, sannan ya bayyana fatansa na ci nasara a yakin da al'ummar kasar ke yi da dakarun kawancen larabawa da Amurka.

Tun a 2015 ne dai sojojin na kasar Saudiyya suka fara kai hari akan kasar Yemen tare da cikakken goyon bayan Amurka, wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci fiye da rayuka 12,000 bisa kididdigar Majalisar Dinkin Duniya.

Tags

Ra'ayi