Sep 21, 2018 12:01 UTC
  • Yemen Ta Bukaci Duniya Ta Dorawa Saudiyya Alhakin Yaki

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Yemen ta kira yi kungiyoyin kasa da kasa da su dorawa Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa laifin kallafawa mutane Yemen yaki da kuma laifukan da ke tattare da shi.

Kamfanin dillancin labarun "Saba'a" na Yemen ya ambato ma'aikatar harkokin wajen gwamnatin ceton kasa da ke San'aa na mayar da martani akan wasikar da jakadiyar Hadaddiyar Daular Larabawa ta aike wa kwamitin tsaro yana mai dorawa Yemen rushewar tattaunawar Geneva.

Ma'aikatar harkokin wajen ta Yemen ta ce; Abin da jakadan kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, Lana Zakiy Nusaibah ta bayyana ba shi da tushe domin kasarta da kuma Saudiyya ne su ka hana wakilan Yemen halartar tattaunawar.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Yemen ta zargi Kasashen na Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da kokarin wasa da hankulan kungiyoyin kasa da kasa akan hakikanin abin da yake faruwa na yakar kasar Yemen.

A ranar 6 ga wtaan Satumba ne aka tsara tattaunawa tsakanin dukkanin bangarorin da suke da hannu a yakin na Kasar Yemen, a birnin Geneva, sai dai Saudiyya ta hana tawagar San'aa tashi daga filin saukar jiragen sama na kasa da kasa a birnin.

Tags

Ra'ayi