• Hizhubullah:Akwai Hannun Shaidanu A Harin Ta'addancin Ahwaz

Cikin wata sanarwa da ta fitar a daren jiya assabar kungiyar hizbullahi ta kasar Labnon ta yi Allah wadai kan harin ta'addancin da aka kai birnin Ahwaz na kudu maso yammacin kasar Iran.

Da farko kungiyar ta hizbullahi ta meka ta'aziyarta ga jagoran juyin juya halin musulinci, gwamnati da al'ummar Iranda kuma iyalen wadanda lamarin ya rusa dasu gami da kuma fatan samun sauki ga wadanda suka raunana, sannan ta ce shakka babu a kwai hanun shaidanun mutane dake kokarin zagon kasa ga tsaron jamhoriyar musulinci ta Iran.

Kungiyar ta ce wannan ta'addanci na a matsayin mayar da martani kai tsaye na nasarorin da kungiyoyin gwagwarmaya na kasashe daban daban ke samu a filin daga.

Har ila yau kungiyar ta Hizbullahi ta tabbatar da cewa wannan ta'addanci ba zai tasiri ba ga gudumuwar da jamhoriyar musulinci ke bayarwa ga kungiyoyin gwagwarmaya da al'ummar Palastinu da sauren al'umomi masu 'yanci da kuma raunana na Duniya.

Tags

Sep 23, 2018 06:43 UTC
Ra'ayi