Oct 21, 2018 06:24 UTC
  • Siriya Ta Bukaci MDD Ta Binciki Kisan Mutane 60 Wanda Amurka Ta Yi A Dair-Zur

A wasu hare-haren da jiragen yakin kasar Amurka suka kai kan kauyuka biyu na kasar Siriya akalla mutane 62 ne suka rasa rasukansu a yayinda wasu da dama suka ji rauni.

Tashar talabijin ta Rasha today ta bayyana cewa Amurka ta kai hare-haren ne a kauyukan Susse da kuma Bubranda a lardin Dair-Zur inda ta kashe fararen hula fiye da 60. 

Gwamnatin kasar Siriya ta yi allawadai da hare- haren sannan ta bukaci MDD ta gudanar da bincike kan hare-hare. Gwamnatin ta kara da cewa hare-haren na lardin Dair-Zur sun nuna cewa gwamnatin Amurka ba ta zo kasar Siriya don yakar yan ta'adda ta Daesh kamar yadda take riyawa ba. Banda haka ta ce Amurka na taimakawa wadannan kungiyoyin yan ta'adda, sannan tana kashe fararen hula wadanda basu yi wani laifi ba. 

A jiya Asabar ne dai ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Siriya ta ce ta mika wannan koken a rubuce ga majalisar dinkin duniya don daukar matakan da suka dace. 

Sojojin kasar Amurka sun shiga kasar Siriya ne tun shekara ta 2014 da sunan yaki da kungiyar yan ta'adda ta ISIS ko Daesh, sannan tana aiki da wasu kungiyoyin yan ta'addan don ganin bayan gwamnatin shugaban Bashar Al-asad tun lokacin. 

Kafin haka dai gwamnatin kasar Amurka ta bayyana cewa ba za ta bar kasar Siriya ba sai lokacinda ta ga ba wani sojan kasar Iran da ya rage a kasar Siriya. Iran ta shiga kasar Siriya ne tare da bukatar gwamnatin kasar.  

 

Tags

Ra'ayi