Nov 01, 2018 17:05 UTC
  • MDD: Sama Da Kananan Yara Miliyan 7 Ne Suke Fuskantar Barazanar Yunwa

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewar sama da kananan yaran kasar Yemen miliyan 7 ne suke fuskatar gagarumar barazanar yunwa a kasar sakamakon ci gaba da hare-haren wuce gona da irin da Saudiyya da kawayenta suke ci yi a kasar.

Babban daraktan yankin Gabas ta tsakiya da Arewacin Afirka na kungiyar ta UNICEF, Geert Cappelaere ya bayyana hakan inda yace: A halin yanzu  kimanin yara miliyan 1.8 'yan kasa da shekaru biyar ne suke fuskantar yanayin rashin abinci na tsaka tsaki, sannan wasu kimanin 400,000 kuma suke fuskantar tsananin rashin abinci a kasar ta Yemen.

Har ila yau jami'in na UNICEF ya ce sama da rabin mutane miliyan 14 da suke fuskantar matsalar yunwa a kasar Yemen yara kanana ne, inda yayi kiran da a kawo karshen yakin da kuma daukar matakan da suka dace wajen kula da yara da sauran al'ummar kasar ta Yemen.

A cewar jami'in na MDD tun bayan da aka kaddamar da wannan yakin, sama da mutane 6000 ne aka kashe su ko kuma  suka sami raunuka masu tsananin gaske.

 

Tags

Ra'ayi