Nov 07, 2018 19:04 UTC
  • Yahudawan Sahyuniya Sun Kutsa Cikin Masallacin Aqsa

Yahudawan sahyuniya sun kutsa kai a cikin masallacin Aqsa mai alfarma tare da keta alfarmar masallacin mai daraja.

Kamfanin dillancin labaran Mehr ya bayar da rahoton cewa, wani malamin yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra'ayi, ya jagoranci gungun wasu yahudawa inda suka kutsa kai cikin masallacin quds mai alfarma.

Yahudawan dai sun isa wurin ne da nufin tsokanar musulmi, a daidai lokacin da kuma suke samun cikakkiyar kariya daga jami'an tsaron Isra'ila da suke dauke da makamai.

Masu gadin masallacin quds dai ba su ce da su uffan ba, amma dai sun rufe dukkanin kofofin massalacin, inda yahudawan suka tsaya a cikin harabar masallacin.

Tags

Ra'ayi