Nov 14, 2018 19:26 UTC
  • Ministan Yakin Isra'ila Ya Yi Murabus Daga Kan Mukaminsa

Ministan yakin Isra'ila Avigdor Lieberman ya yi murabus daga kan mukaminsa

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, Ministan yakin Isra'ila Avigdor Lieberman ya yi murabus daga kan mukaminsa ne sakamakon dakatar da bude wuta a Gaza, inda yake kallon hakan a matsayin gazawa ga gwamnatin Netanyahu.

Avigdor Lieberman ya ce ajiye mukaminsa kuma jam'iyyarsa ta fice daga hadakar da ke mulki a karkashin Netanyahu, domin kuwa a cewarsa abin da ya faru abin kunya ne ga gwamnatin Isra'ila, ta yadda Falastinawa suka tilasta mata dakatar da bude wuta, duk kuwa da ruwan makamai masu linzami da suka yi a kan gidajen yahudawa.

Falastinawa suna kallon ajiye mukamin da Avigdor Lieberman ya yi, ya tabbatar da irin raunin da kuma gagarumar barakar da ke tsakanin gwanatin Isra'ila.

 

Ra'ayi