Nov 16, 2018 06:37 UTC
  • Hamas: Amurka Tana Kokarin Rusan Jagororin Palasdinawa

Kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas ta bayyana haka ne a yayin da take mayar da martani akan shigar da sunan daya daga jagororinta cikin sunayen 'yan ta'adda

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar bayani da ya kunshi bayyana Sheikh Salih Aruri a matsayin dan ta'adda tare da ware dalar Amurka miliyan 5 ga duk wanda ya ba da labari akansa.

Wani jami'i mai magan da yawun kungiyar ta Hamas, Husam Badran ya fada a jiya alhamis cewa; Shigar da sunayen jagororin kungiyar a cikin jerin sunayen 'yan ta'adda a idon Amurka, ba zai sauya komai ba dangane da siyasar kungiyar gwgawarmayar.

Shi dai Salih Aruri yana a matsayin mataimakin shugaban kungiyar ta Hamas ne

Ita ma kungiyar Jihadul-Islami ta Palasdinu ta bayyana cewa Amurkan ta dauki wannan matakin ne a daidai lokacin da 'yan sahayoniya su ke kashe palasdinawa da makaman da Amurka ta kera

Tags

Ra'ayi