Dec 08, 2018 18:18 UTC
  • Sojojin HKK Suna Kusantar Kan Iyakar Kasar Lebanon

Tashar talabijin al-alam ya bada labarin cewa; Sojojin na haramtacciyar Kasar Isra'ila sun girke wasu na'urori na zamani masu hangen nesa akusa da garin Meis Jabal na Lebanon

Bugu da kari sojojin na haramtacciyar Kasar Isra'ila sun harba bindigogi a cikin iska lokacin da sojojin Lebanon su ka karaci kan iyaka domin gudanar da aikin tsaro.

Kakakin sojojin Sahayoniya Avichay Adraee ya riya cewa; Sojojin sun harba bindiga ne domin gargadin mayakan Hizbullah akan iyaka.

Kwanaki biyu da suka gabata ne sojojin na haramtacciyar kasar Isra'ila su ka fara gudanar da abin da su ka kira aikin gano ramukan karkashin kasa da Hizbullah ta gina, wadanda su ka shiga cikin yankin palasdinu da yake karkashin mamaya

A ranar Talatar da ta gabata, sojojin na haramtacciyar Kasar Isra'ila sun sanar da gano wani rami mai tsawon mita 400 da su ke ce HIzbullah ta gina a kusa da kauyen Kafar Kalla.

Tuni dai kungiyar Hizbullah a Lebanon ta gargadin haramtacciyar Kasar ta yahudawa da kada su wuce gona iri, domin za su fuskanci mayar da martani mai tsanani

Tags

Ra'ayi