Dec 08, 2018 18:20 UTC
  • Ansarullah Ta Bayyana Kudurinta Na Ganin Zaman Lafiya Ya Tabbata A Kasar Yemen

Daya daga cikin masu wakiltar kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen da aka fi sani da 'yan Huthy, ya bayyana cewa; Sun je kasar Sweeden ne domin ganin an samu zaman lafiya a Yemen

Abdulmalik al-ajzy ya kuma yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su taimaka a aikace domin ganin tattaunawar sulhu da ake yi tsakanin bangarorin kasar Yemen, ta kai ga samun nasara.

al-Ajzy ya kara da cewa; Masu yakar kasar Yemen sun hau kan teburin tattaunawa ne bayan da su ka sha kashi a fagen daga, don haka da akwai shakku akan tsarkin niyyar Amurka na kawo karshen yaki.

Dan tawagar tattaunawar na Ansarullah ya kuma bayyana cewa; A yanzu da aka shiga kwana na biyu ana tattaunawar ba za a iya cewa an cimma wata matsaya ta azo a gani ba.

A ranar shida ga watan nan na Disamba ne aka bude tattaunawar sulhu a tsakanin bangarorin da suke yaki da juna a kasar ta Yemen, a kasar Sweeden bisa shiga tsakanin Majalisar Dinkin Duniya.

Saudiyya ta shelanta yaki ne akan kasar Yemen tun a 2015 wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci rayuka fiye da 13,000 yayin da wasu dubu dubatar suka jikkata.

Bugu da kari yakin ya lalata asibitoci da cibiyoyin shan magani na kasar,kamar kuma yadda ya jawo bullar yunwa da cutar kwalara.

Tags

Ra'ayi