Dec 09, 2018 06:48 UTC
  • Bin Salman Ya Yi Batan Dabo Tun Bayan Da Ya Bar Aljeriya

Tun bayan da yariman Saudiyya mai jiran gadon sarautar kasar Muhammad Bin Salman ya bar kasar Aljeriya a ranar 4 ga wannan wata na Disamba, har yau ba a kar ajin duriyarsa ba.

Kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya WAS ya bayar da rahoton cewa, Muhammad Bin Salman ya bar kasar Aljeriya tun ranar 4 ga watan Disamba, ba tare da bayyana inda ya nufa ba.

Wannan batan dabo da yariman ya yi ya jawo shakku kan abubuwa da dama dangane da batun yarima, wanda yake fuskantar matsin lamba a cikin kasar ta Saudiyya dama a kasashen duniya, musamman tun bayan kisan Jamal Khasoggi wanda ake zargin yariman da hannu kai tsaye cikin lamarin, da kuma kisan kiyashin da yake yi kan al'ummar kasar Yemen.

Bin Salman ya halarci taron kasashen G20 a Argentina, inda ya fuskanci kauracewa daga shugabannin kasashen duniya, daga nan kuma ya ziyarci wasu kasashen larabawan yankin Magrib, inda a can ma ya fusknaci zanga-zangar yin tir da Allawadai da ziyarar tasa, bisa tsarin tafiyarsa dai zai wuce kasar Jordan ne daga Aljeriya, amma daga lokacin da ya bar Aljeriya ba a bayyana inda ya nufa ba kuma ba a kara jin duriyarsa ba har zuwa yau.

Ra'ayi