Dec 15, 2018 06:31 UTC
  • Iraqi Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Ta Sama Wanda Turkiya Ta Kai Cikin Kasar

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iraqi ta bada sanarwan cewa ta kira jakadan kasar Turkiya a Bagdaza don gabatar da korafinta kan hare-haren keta hurumin kasar wanda gwamnatin kasar Turkiyya ta yi a jiya Alhamis.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wani rahoton da ma'aikatar ta fitar a jiya jumma'a wanda yake cewa"Gwamnatin kasar Iraqi tana Allawadai da hare-haren da jiragen yakin kasar Turkiya suka kai yankunan kurdawan kasar a ranar Alhamis da ta gabata".

Ma'aikatar ta kara da cewa hare-haren ba tare da neman amincewar bagdaza ba keta hurumin kasar ne sannan keta hurumin yan kasar ta Iraqi ne. Mutane da dama ne suka rasa rayukansu a hare-haren da Ankara ta kai a arewacin kasar Iraqi da sunan murkushe mayakan kungiyar kurdawa ta PKK a yankin.

Sojojin kasar Turkiya sun tabbatar da cewa sun kashe mutane 8 daga cikin mayakan PKK a yankunan Zap, Hakurk da kuma Haftain a arewacin kasar ta Iraqi.

 

Tags

Ra'ayi