Dec 15, 2018 19:28 UTC
  • Palasdinawa Da Dama Sun Jikkata A Yankin Yammacin Kogin Jordan

Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila Sun Jikkata Palasdinawa masu yawa a yammacin Kogin Jordan

Sojojin na haramtacciyar kasar Isra'ila da suke kokarin rusa gidan Abu Hamid da ke sansanin 'yan gudun hijira na al-am'ary a garin Birah, sun jikkata mutane 56 da su ka yi zaman dirshan a gidan domin hana su taba shi. Da akwai 'yan jarida 3 a cikin wadanda su ka jikkata

Har ila yau sojojin 'yan sahayoniyar sun kame wasu Palasdinawan da suka dai 100 a kusa da gidan da su ka rsuhe

A gefe daya, an ci gaba da yin taho mu gama a tsakanin 'yan sahayoniya da kuma samarin Palasdinawa a yankin na yammacin kogin Jordan wanda ya fara tun jiya juma'a har zuwa safiyar yau Asabar

Da akwai Palasdinawa 6500 da suke tsare a gidajen kurkukun yahudawa, daga cikinsu da akwai kananan yara 350 da mata 62

Tags

Ra'ayi